Da Dumi Dumi

An dage wasa a filin wasa na garin Uyo har sai baba- ta -gani

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da sanarwar rufe filin wasa na garin Uyo da ke Jihar Akwa Ibom har sai baba-ta-gani.
Kafar sadarwar bayar da labaran wasanni ta Supersport.com ta ruwaito cewa rufe filin wasan ba ya rasa nasaba da yadda magoya bayan kulob din Akwa United suka wulakanta alkalan wasa a lokacin da wasa ke gudana a tsakanin kulob din da na Warri Wolbes a makon da ya gabata.
Rahoton ya ce alkalin wasa Henry Ogunyamodi tare da masu taimaka masa sun tsayar da wasan ne jim kadan da dawowa hutun rabin lokaci ganin yadda magoya bayan kulob din suka rika jifansu da kuma antaya musu bakaken maganganu.
A lokacin da aka tsayar da wasan, kulob din Akwa United ne ke gaba da ci 2-0 bayan da ’yan wasa Ubong Ekpai da Emmanuwl Erinze suka zura kwallaye a ragar Warri Wolbes.
Sai dai da wannan dagewar, hukumar ta zaftare maki uku da kwallaye uku daga makin da kulob din Akwa United ya hada a gasar  a matsayin hukunci sannan tuni ta umarci kulob din ya biya alkalan wasan Naira dubu 200 kowannensu.   Haka kuma ta ce kulob din ne zai dauki alhakin gyara abubuwan da aka lalata a daukacin filin wasan ba tare da bata lokaci ba..
Yanzu kulob din zai rika buga wasansa na gida ne a filin wasa na Rojeney da ke garin Oba kusa da Onitsha har a kare kakar wasa ta bana.