✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage zaman majalisar dattawa saboda karancin Sanatoci

A yau Talata ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun dage zaman majalisar da aka saba yi sakamakon karancin Sanatocin da basu halarci zauren majalisar. Kasa da…

A yau Talata ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun dage zaman majalisar da aka saba yi sakamakon karancin Sanatocin da basu halarci zauren majalisar.

Kasa da Sanatoci 20 ne suka halarci zauren majalisar dattawan. A ranar Alhamis data gaba ta ne Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Sanata Phillip Aduda ya gabatar da dokar majalisar ta sashi na 10 sakin layi na 3 da ke cewa, majalisar ba zata iya aiwatar da doka ba idan basu kai adadin Sanatoci 38 a zauren majalisar.