Da Dumi Dumi

An daina sanya siyasa kan matsalolin Fulani a Najeriya

Shugaban kungiyar Matasan Fulani da Aldodi, Malam Abdulkarim Bayero ya ce ana siyasantar da matsalolin da suka addabi Fulani a kasar nan.

A cewarsa, ’yan siyasa suna amfani da matsalar rashin tsaro da ke faruwa a yankunan Fulani suna satar kudi da sunan samar da tsaro. Ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.

Ya ce hakika a cikin kowace al’umma akwai batagari kuma akwai barayi amma yadda ake danganta Fulani kadai da miyagun ayyuka abin damuwa ne.

Ya ce Fulani mutane ne masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar kowa a kasar nan. “Mu Fulani ba masu son tashin hankali ba ne, muna kuma da ’yanci kamar kowa da kuma son mu yi kiwon dabbobinmu a ko’ina a kasar nan kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Mu masu bin dokokin kasa ne kuma a kowace al’umma akwai marasa gaskiya, ana kuma samun barayi amma zancen Fulani an mayar da shi siyasa,” inji shi.

Ya ce ’yan siyasa na satar kudin kasa da sunan samar da tsaro saboda batun Fulani. “Saboda haka muka hadu domin tattauna yadda za mu ga cewa nan gaba duk wanda zai shugabanci kasar nan sai wanda muka yarda zai yi mana adalci za mu zaba,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa Fulani ba za su yarda su sake zaben wani shugaba ba tun daga matakin kansila zuwa Shugaban kasa sai mai adalci. “Akwai shirin da muke yi na ganin mun wayar wa sauran Fulani kai su tabbatar duk inda suke wanda za su zaba a zabe mai zuwa sai wanda zai yi musu adalci,” inji shi. Ya ce tuni Fulani suka yi rajistar katin zabe kuma ba kowa za su zaba ba sai wanda ya san mutuncinsu a kasar nan.

A jawabin Sakataren kungiyar Abdulrahman Ibrahim Muhammed ya ce an mayar da Fulani saniyar ware a kasar nan.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya