✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da Deco daga buga kwallo na tsawon shekara guda a Fotugal

Tsohon dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen da kuma kulob din Chelsea da ke Ingila Deco ya shiga halin ni-’yasu bayan da kotun da…

 Deco, tsohon dan kwallon FC Barcelona da ChelseaTsohon dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen da kuma kulob din Chelsea da ke Ingila Deco ya shiga halin ni-’yasu bayan da kotun da ke hukunta ’yan kwallo a Fotugal ta same shi da laifin amfani da kwayoyin kara kuzari a lokacin da yake buga kwallo inda ta zartar masa da hukuncin daina yin wasa har na tsawon shekara guda.
Tun a watan Maris kotun take zarginsa da laifin yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari . A wancan lokaci kotun ta yanke masa hukuncin wata guda ne kafin ta kammala bincike.  Sai dai a ranar Alhamis ta makon jiya kotun ta tabbatar da laifinsa kuma ta zartar masa da hukuncin daina buga kwallo na tsawon shekara guda.  
dan asalin Fotugal, Deco ya fara yin suna ne a kulob din FC Porto da ke Fotugal a shekarar 2004 a karkashin horarwar koci Jose Mourinho bayan da kulob din ya lashe gasar zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League).  Daga nan ya koma kulob din FC Barcelona inda ya sake samun nasarar lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a karo na biyu da kuma kofin La-Liga sau biyu kafin ya canza sheka zuwa kulob din Chelsea da ke Ingila a shekarar 2008.
Bayan ya shafe shekara biyu a Ingila yana wasa sai ya koma kasar haihuwarsa watau Fotugal inda ya koma kulob din Fluminense a shekarar 2010.
Sai dai kafin kotu ta yanke wannan hukunci, tuni Deco ya bayar da sanarwar ya daina buga kwallo a rayuwarsa, watau dai ya yi ritaya.
Don haka masana harkar kwallo na ganin wannan hukunci ba zai yi tasiri a kansa ba, tun da ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda.