Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An damke mutumin da ya kashe iyalansa

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

An damke mutumin da ya kashe iyalansa

Al’ummar Karamar Hukumar Odo Otin da ke Jihar Osun sun kasance cikin zullumi bayan da aka kama wani mutum da kashe matarsa da ‘ya’yansa biyu. 

Ana zargin mutumin ya sanya adda ya daddatsa matarsa da ‘ya’yansa biyu ya kuma sassari jikinsa domin ya boye laifinsa, inda ya yi yekuwar cewa wani ne ya kai farmaki ga shi da iyalan nasa. 

Sai dai jami’an ‘yan sanda masu binciken farko sun ce mutumin ne ya kashe iyalansa, kuma sun gano addar da ya yi amfani da ita a gidan. 

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola ta tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ta ce rundunar kan binciken a kai.