✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dauki matasa dubu 400 aiki a shirin inganta rayuwa – Minista

Gwamnatin Tarayya ta dauki matasa dubu 473 da 137 a karkashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu. Wani rahoto da kafar labarai ta Premium Times ta…

Gwamnatin Tarayya ta dauki matasa dubu 473 da 137 a karkashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu.

Wani rahoto da kafar labarai ta Premium Times ta buga ya ce Ministar Ayyukan Jinkai da Yaki da Annoba da Inganta Rayuwar Jama’a, Hajiya Sadiya Umar ce, ta bayyana haka.

Hajiya Sadiya Umar ta yi wannan bayani ne lokacin da Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da Shirin Yaki da Fatara da ya kai mata ziyara a ofishinta.

Ministar ta ce tun farko an kirkiro Shirin N-Power ne kacokan domin samar wa matasa ayyukan yi.

Cikin watan Fabrairu  Premium Times ta buga labarin wani garambawul din da Ma’aikatar Ayyukan Agaji da Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma ta ce za ta yi wa shirye-shiryen NSIP.

“An kirkiro N-Power ne don inganta rayuwar matasa, ta hanyar sama musu ayyukan yi ta yadda za a habaka fannonin ilimi da noma da lafiya da kuma haraji. Kudirin wannan gwamnati shi ne a sama wa matasa akalla dubu 500, ayyukan yi a  kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan,” inji Ministar.

Ta yi karin bayani a kan shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma ta hanyar ba su lamunin kama sana’o’in yau da kullum domin dogaro da kai.

Ta ce har yanzu gwamnati na ci gaba da bayar da tallafin rage radadin talauci na Naira 5,000 da ake rabawa duk wata ga marasa galihu.

A jawabin Shugaban Kwamiti, Abdullahi Silame, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, saboda ci gaba da gudanar da shirin da take yi.