✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure lauyan bogi shekara biyu

Kotun Majistare ta 35 da ke Nomanslan a Kano ta daure wani mai suna Prince Ekele bisa zarginsa da yin sojan gona cewa shi lauya…

Kotun Majistare ta 35 da ke Nomanslan a Kano ta daure wani mai suna Prince Ekele bisa zarginsa da yin sojan gona cewa shi lauya ne.

Tun farko ’yan sanda ne suka gurfanar da Mista Ekele a gaban kotun inda suke tuhumarsa da sojan gona yane sa kayan aikin lauya yana zagayawa kotuna daban-daban da manyan litattafai a hannunsa yana kuma kare wadanda ake tuhuma a matsayin shi lauya ne.

Koda aka karanta masa laifin da ake zarginsa, Mista Ekele bai musanta ba, inda ya nemi sassaucin kotu a kan huncin da za ta yi masa.

Alkalin kotun Mai shari’a Sanusi Usman Atana ya tambayi mai gabatar da kara a kotun ASP Nura Mukhtar ko an taba gurfanar da Mista Ekele gaban wata kotu kan wannan laifi, inda mai gabatar da karar ya ce akwai tuhumar da aka yi masa a kan zamba cikin aminci.

Sai Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin wata 20 a kurkuku ba tare da zabin tara ba.