✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure mai fyade shekara 16

Babbar Kotun Jihar Kano ta 2 ta yanke wa wani magidanci mai suna Auwalu Abdullahi mazaunin Unguwar Ja’en Makera a Karamar Hukumar Kumbotso hukuncin daurin…

Babbar Kotun Jihar Kano ta 2 ta yanke wa wani magidanci mai suna Auwalu Abdullahi mazaunin Unguwar Ja’en Makera a Karamar Hukumar Kumbotso hukuncin daurin shekara 16 a kurkuku bisa samunsa da laifin yi wa wani karamin yaro fyade, inda ya janyo yaron ya shiga wani mugun hali.

Alkalin Kotun Mai shari’a A’isha Rabi’u Danlami ta ce laifin da ake zargin Auwalu da aikatawa laifi ne da ya saba wa sashe na 284 na Kundin Final Kod.

Mai shari’a A’isha Danlami ta kuma cewa mai gabatar da kara Amina Yusuf ’Yargaya ta gabatar da shaidu hudu kwarara don haka kotun ta samu wannan matashi da laifi don haka ne ta yanke masa hukuncn daurin shekara 16 tare da aiki mai tsanani.