✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure mai sayan abinci da sarka saboda kar ya gudu bai biya ba

A wani rahoton hoto da ake ta yadawa wanda ya janyo muhawara a shafukan sada zumunta a gidan cin abinci a kasar Peru, an bayyana…

A wani rahoton hoto da ake ta yadawa wanda ya janyo muhawara a shafukan sada zumunta a gidan cin abinci a kasar Peru, an bayyana wani matafiyi dan kasar Benuzuela da aka daure shi da sarka lokacin da yake cin abinci don gudun kar ya tsere bai biya kudin abincin da ya ci ba.

Asalin hoton an wallafa shi ne a shafin Tiwita na wani dan jaridar kasar Benuzuela mai suna Luis Martinez, wanda ya yi rubutu game da mai sayan abincin da ka yi wa lakabi da La Patilla.

A lokacin da aka wallafa rubutun a wasu shafukan yanar gizo ake iya karantawa, an cire hotunan a shafin dan jarida Luis. Ana tuhumar dan jaridar ne akan samun hoton wani matafiyi dan kasar Peru da ya bar kasar sanadiyyar wasu matsaloli daga Benezuela. A cikin rubutun da dan jaridar ya goge a shafinsa na Tiwita, na bayyana cewa La Patilla ne da kansa ya daure jikinsa da sarka lokacin da yake zaune yana cin abinci amma ya sakaya fuskarsa saboda gudun abin da zai biyo baya a kasar Peru.

La Patilla, na bayyana wannan hoton a matsayin wata alama da ke nuna kabilanci da ake yi wa baki ’yan kasar Benezuela, wanda suke zaune a kasar, musamman ’yan kasashen Kolombiya, Brazil da Peru. Sai dai a wani bangaren wanda ya mallaki gidan abincin ya yi hakan ne, don tabbatar da cewa mutumin bai fita daga gidana abincin ba har sai ya biya kudin da yaci abincin.

Mafi yawan masu karatu sun yi ta sukar rubutun Luis akan cewa, ba kowa bane zai amince da irin cin mutucin da aka yi wa La Patilla wajen fallasa shi a shafukan sada zumunta ba.

A wani rubutu da dan jaridar ya sake wallafawa na cewa, La Patilla bai san za a daure shi da sarka ba, lokacin da yake zaune ba har ya dauki hoton kansa a matsayin shaida daga bisani ya fita daga gidan cin abincin. Ya kuma tabbatar da rahoton da dan jaridar ya wallafa a shafinsa na Tiwita gaskiya ne.

Luis, ya ce a yanzu haka ina tattara bayanai game da rahoton da wasu jama’a da suke kokonto akan sahihincin rahoton da na wallafa.

An dai sakaya sunan hoton da aka wallafa, don kauce wa cin mutunci. Wanda aka daure da sarkar ya bayyana cewa bai da masaniya a kan abin da zai same shi, har sai da ya zauna, ya dauki hotonsa ya tashi daga inda yake zaune ba tare da ya ci abincin ba. Ya ki bayyana sunan gidan abincin saboda yana son ya kammala tattara korafin da zai sanar game da abin da aka yi masa.