✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure Mataimakin Hedimasta shekara 14 kan yi wa dalibarsa fyade

Bababr Kotun Jihar Kano Mai lamba 19 da ke zama a Bompai ta yanke wa Mataimakin Hedimastan Makarantar Firamaren ’Yantama da ke karamar Hukumar Doguwa…

Bababr Kotun Jihar Kano Mai lamba 19 da ke zama a Bompai ta yanke wa Mataimakin Hedimastan Makarantar Firamaren ’Yantama da ke karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano mai suna Shu’aibu Ibrahim da ke zaune a  Unguwar Gangare daurin shekara 14 bisa samunsa da laifin yi wa dalibarsa ’yar kimanin shekara 8 fyade.
Tunda farko masu gabatar da kara sun shaida wa kotun cewa kafin Mataimakin Hedimastan ya yi wa yarinyar fyade sai da ya yi amfani da dan kwalinta ya rufe mata baki tare da barazanar zai kashe ta matukar ta yi masa ihu.
Lauyan Gwamnati Barista Fa’iza Abdullahi ta gabatar wa kotun shaidu guda shida, yayin da lauyan wanda ake zargi Barista Sulaiman Badamasi ya gabatar wa kotun shaidu biyu, sannan wanda ake zargin ya kare kansa a gaban kotun.
Da take yanke hukunci alkalin kotun Mai shari’a Hadiza Sulaiman ta ce kotun ta yanke wa Mataimakin Hedimastan hukuncin daurin shekara 14 ne saboda rashin imanin da ya nuna a kan karamar yarinyar wacce aka damka amanarta a hannunsa.