✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure matar da ta kashe dan uwanta kan naman miya shekara 14

A ranar Litinin da ta gabata ce wata kotu da ke Legas ta daure wata mace mai shekara 34 mai suna Janet James da ke sayar…

A ranar Litinin da ta gabata ce wata kotu da ke Legas ta daure wata mace mai shekara 34 mai suna Janet James da ke sayar da abinci shekara 14 a kurkuku bayan samunta da laifin lakada wa dan uwanta mai shekara 8 duka har ya rasu saboda zarginsa da cinye mata naman miya.

An ruwaito cewa a watan Agustan shekarar 2009 da misalin kafe 8 na dare a Unguwar Ilupeju da ke Jihar Legas ce Janet ta daki dan u’wanta mai suna Sabiour James da rodi bisa dalilin satar naman miya.

Ta ce ta yasar da gawar dan uwan nata a harabar wani kamfanin inshora da ke Unguwar Ilupeju bayan ta aikata laifin.

A bayanin da ta yi wa ’yan sanda Janet ta ce ta gargadi Sabiour a kan ya daina halin bera kafin ta kai ga dukansa, inda ta ce ba nan take ya mutu ba. Ta ce sai bayan da ta tashi cikin dare za ta yi fitsari ta lura Sabiour yana fitar da kumfa ta bakinsa inda ta yi kokarin ceto shi amma abin ya ci tura.

A yayin da take tabbatarmata da laifinta AlkalinKotun Mai shari’a Adebayo Akintoye ta ce ta lura wacce ake kara ba ta wahalar da kotu ba sannan ta nuna nadamarta a kan laifin da ta aikata.

Alkalin Kotun ta hori mai laifin kan ta canja dabi’unta bayan wa’adin da aka yanke mata na zaman gidan yari.

Ta ce wa’adin zai soma aiki ne tun daga 22 ga Agustan 2009 lokacin da Kotun Majistare ta tsare Janet.

Alkalin ta bayyana cewa bisa la’akari da abin da ya faru ta samu Janet da laifin kisan kai a karkashin sashi na 337 na Kundin Manyan Laifuffuka na Jihar Legas.

Alkalin ta ce “Na gamsu da bukatar wacce ake kara da mai kare ta suka gabatar ta neman a yi mata sasauci, saboda nuna nadama da rashin wahalar da kotu bayan ta kasance a tsare a kurkuku na shekaru da dama. Saboda haka wacce ake kara Janet James kotu ta yanke mata hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari. Lokacin daurin zai soma aiki ne tun daga 22 ga watan Agustan 2013.Wannan shi ne hukuncin kotu,” inji ta.