Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An daure yarinya kan satar Naira miliyan 3.5

Sufeto Janar Adamu Abubakar Muhammad
Sufeto Janar Adamu Abubakar Muhammad

Kotun Majistare ta 15 da ke Kano ta daure wata yarinya ’yar shekara 13 sakamakon samunta da laifin  sace wa marikinta Naira miliyan uku da rabi.

Tun farko dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Jacob Yaduma ya shaida wa kotun cewa wani dan kasuwa mai suna Mista Olayinka Dagunduro da ke Unguwar Zangeru a Sabon Gari Kano ya yi karar Misis Shola Ogedegbe da ke Unguwar Otudola a Sabon Gari, wacce ita ce shugabar makarantar da ’ya’yansa suke karatu; inda ya zarge ta da karbar kudin da ’yar rikonsa ta sace masa.

ADVERTISEMENT

A cewar mai kara, kasancewar idan ya yi ciniki da yamma yakan taho da kudin gida kafin gari ya waye ya kai banki, hakan ya ba ’yar rikon tasa damar kwashe  kudin tare da kai wa shugabar makarantarsu ajiya.

“Na gane cewa idan na ajiye kudi ana daukar mini, sai dai ban gano mai dauka ba, har sai ranar wata Lahadi na ajiye Naira miliyan biyu da rabi a dakina na tafi coci. Bayan na dawo ban ga kudi ba na fara bincikar mai aikina, inda ta gaya min cewa Serah ta shigo gidan ta ce mata wai ni na aiko ta ta dauki sako a dakina ta kai mini coci. Hakan ya sa na tsananta bincike a kan Serah ta gaya min gaskiyar yddda aka yi ta dauki kudin da kuma wacce ta kai mawa.”

ADVERTISEMENT

Sai dai yarinyar da ake zargi (wacce aka boye sunanta) ta amsa laifuffukanta na ketare iyaka da balle kofa da sata, wadanda suka karya dokoki na 342 da 346 da317 na Kundin Shari’a na Final Kod.

Ta bayyana wa kotun cewa shugabar makarantarsu ce ta sanya ta aikata haka, inda ta yi mata alkawarin tara mata kudin satar da nufin tura ta karatu kasar waje. “A lokuta daban-daban na dauko kudi a dakin marikina, inda nake kai wa shugabar makarantarmu saboda ta yi min alkawarin za ta yi kasuwanci da kudin yadda za a samu ribar da za ta kai ni karatu kasar waje,” inji ta

Da aka waiwayi shugabar makarantar, ta musanta laifin da ake zarginta da shi na karbar kayan sata, wanda ya saba da sashe na 352 na Kundin Final Kod.

Alkalin Kotun, Mai shari’a Mukhtar Dandago ya yanke wa dalibar hukuncin daurin shekara guda ko zabin biyan tarar Naira dubu 50. Daga nan ya dage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan nan, don ci gaba da sauraren shaidu dangane da bangaren shugabar makarantar.