Da Dumi Dumi

An dawo da ‘Yan Najeriya 315 daga Afrika ta Kudu a karo na biyu

Da misalin karfe 8 na daren jiya Laraba ne jirgin ‘Air peace’ kirar boyin 777 mai lamaba 5N-BWI ya sauka a filin sauka da tashin jirage na kasa na Murtala Muhammad da ke Ikeja a Legas dauke da ‘yan Najeriya 315 wadanda suka hadar da manya 290 da yara 25 da aka yo jigilar su daga kasar Afirka ta Kudu zuwa gida Najeriya.  

Tun a ranar Talata ake sa ran jigilar ‘yan Najeriyan a karo na biyu amma aka samu jinkiri har zuwa daran Laraba sakamakon tsaikon bai wa kamfanin jiragen ‘Air Peace’ izinin sauka kasar Afirka ta Kudu da jami’an kasar suka yi.

Mahukuntan Najeriya sun yanke shawarar kwaso ‘yan kasar da ke Afirka ta Kudu wadanda suka zabi komowa gida tun bayan rikicin nuna kin jinin baki bakaken fata da ya varke a kasar, lamarin da ya yi salwantar rayuka da tarin dukiyoyin bakin a kasar Afirka ta Kudu.

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakai da dama dan nuna bacin ranta bisa lamarin ciki har da janyewar da tayi daga halartar taro na kasa da kasa da ake a kasar Afirka ta Kudun, sai dai a ‘yan kwanakin bayan nan kasar ta Afirka ta Kudu ta nemi afuwa inda ta turo wakilan ta Najeriya wadanda suka gana da shugaba Buhari.

ADVERTISEMENT
Share