✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara binciken satar yaran Kano da samamen ‘yan sanda a makarantar Islamiyya

Majalisar koli ta shari’ar Musulunci a Najeriya ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar batun sace yaran Kano da kuma samamen da ‘yan sanda suka…

Majalisar koli ta shari’ar Musulunci a Najeriya ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar batun sace yaran Kano da kuma samamen da ‘yan sanda suka kai a Makarantar Islamiyya da ke Rigasa a Kaduna‎.

A cewar majalisar kwamitin farko mai membobi 16 ne zai binciki abin da ya faru a Makarantar Islamiyya da ke Rigasa sannan kuma kwamitin na biyu mai membobi 5 shi zai bincike batun satar yaran da aka yi a Kano har aka canza masu suna da kuma addini.

Babban Sakataren Majalisar ta Kasa Nafiu Baba-Ahmad, wanda mataimakinsa Jamilu Mu’azu Hidara, ya wakilta ne ya sanar da hakan a wajen wani taro na musamman da aka yi da makamai da limamai a jihar Kaduna.

Ya ce, majalisar zata bayyawa duniya gaskiyar abin da ‎ya faru a makarantar Islamiyya ta Rigasan idan kwamitin sun kammala aikinsu.

‎”An kafa kwamitin ne domin duba zarge’zargen da aka rika yadawa a kasar akan makarantar Islamiyya da kuma zancen satar yaran Kano. Saboda yin adalci ga kowa shi yasa majalisar ta kira wani taro da dukkan kungiyoyin musulunci a hedkwatar Jama’atu Nasril Islam domin tattaunawa.

“Dukkan Kungiyoyin sun samu wakilci a wajen taron. Muka kafa kwamitin bincike mai mutum 16 domin bincikar abin da ya faru a Makarantar Islamiyya ta Rigasa. Sai kuma kwamiti mai mutum biyar su za su bincike batun yaran nan na jihar Kano.

‎” Majalisar zata fitar da sakamakon kwamitin bayan sun kammala aikinsu. Domin binciken su zai nuna gaskiya abin da ya faru a Makarantar ba abin da ake karantawa a kafafen yada labarai ba,” in ji shi.

Majalisar ta kuma yi kira ga malamai da su taimaka wajen wayarwa da jama’a kai akan hadarurrukan da ke tattare da yada labaran karya musamman a shafukan zumunta.

Har ila yau majalisar ta gargadi jama’a musulmi da su ji tsoron Allah a duk inda suke sannan su daina aikata munanan aiyuka da suke aikatawa a boye ko a bayyane.

A jawabinsa, Babban Sakataren Jama’atu Nasril Islam Shaikh Khalid Abubakar Aliyu, ya yi kira ga al’umma su ci gaba da yin alkunuti domin a samu saukin fitittinu da ke addabar kasar nan.

Ya ce, akwai kuma bukatar musulmi su koma ga Allah wajen gudanar da al’amuransu, musamman malaman addini.