✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gasar kwallon kafa na Magajin Garin Jama’a

A ranar Larabar da ta gabata aka fara gasar kwallon kafa na zaman lafiya na Magajin Garin Jama’a inda za a fafata a tsakanin kulob-kulob…

A ranar Larabar da ta gabata aka fara gasar kwallon kafa na zaman lafiya na Magajin Garin Jama’a inda za a fafata a tsakanin kulob-kulob 16 da ke ciki da wajen garin Kafanchan a babban filin wasan da ke garin Kafanchan.

Yayin da yake jawabi a lokacin bude gasar, Magajin Garin Jama’a, Alhaji Abubakar Sadik Muhammad Isa ya yi kira ga kulob-kulob din da za su fafata da su kasance masu kiyayewa tare da bin doka da oda yayin gudanar da gasar, inda ya tunatar da su cewa hatta wadanda suka fi kowa yin fice a harkar kwallo kamar su Messi ana hukunta su idan sun taka doka wanda hakan ke nuni da irin darussan da ke cikin harkar kwallon kafa.

Magajin Garin ya kuma yi kira ga sauran jama’a da su ba da cikakken hadin kai tare da nunawa duniya cewa Masarautar Jama’a ta jama’a ce inda ake zaune lafiya tare da hadin kai a tsakanin kabilu da mabiya addinai daban-daban da ke ciki da wajen masarautar.

Shi ma Ko’odinetan shirya gasar, Alhaji Baballiya Musa, ya ce daga cikin makasudin shirya irin wadannan wasanni akwai kulla dankon zumunci a tsakanin kabilu daban-daban musamman a yankin Kudancin Kaduna kama daga ’yan kwallon har zuwa masu zuwa kallo wanda hakan ke haifar da kyakkyawan zumunci.

Magajin Garin Jama’a Abubakar Sadik Muhammad Isa dan Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II.