Da Dumi Dumi

An fara jigilar ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

Da yammacin nan kashi na farko na ‘yan Najeriya suka taso daga kasar Afirka ta Kudu inda ake sa ran saukar su birnin Legas da misalin karfe 11:15 na daren yau.

Tunda fari dai an sa ran ‘yan Najerian za su sauka filin sauka da tashin jirage na Haji Kamp da ke Ikeja a Legas, amma daga baya aka sami jinkirin isowar su.

Mai taimakawa shugaba Buhari a fannin harkokin kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa, ta shaidawa manema labarai ciki har da wakilin Aminiya cewa jinkirin jigilar ‘yan Najeriyan ya biyo bayan tsaurara bincike da jami’an shige da fice na kasar Afirka ta Kudu suka kara yi akan ‘yan Najeriyan duk da a baya an tantance su, tace tana ci gaba da tuntubar ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar ta Afirka ta Kudu a kan lamarin, inda ta ce zuwa yanzu ta tantance tare da yi wa ‘yan Najeriya mutum 317 rijista wadanda za a dawo dasu gida Najeriya wadanda suka hadar da mata 83 maza 23, tace bata da tabbas ko mutum nawa za su sauka birnin na Legas a yau

Zuwa yanzu manema labarai da jami’an filin sauka da tashin jirage na kasa da na bada agajin gaggawa ta NEMA sun yi zaman dirshen suma sauraron saukar ‘yan Najeriyan daga Kasar Afirka ta Kudu.

‘Yan Najeriya masu jiran saukar ‘yan uwansu daga Afirka ta Kudu

Gwamnatin Najeriya ta yi yunkurin maido da ‘yan kasar ta gida tun bayan barkewar rikicin nuna wariya da ake nuna wa baki bakaken fata a kasar ta Afirka ta Kudu lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dimbin dukiyoyin su.

ADVERTISEMENT
Share