Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An fara shari’ar Alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen

A yau Litinin an fara shari’ar Alkalin alkalan Najeriya mai shari’a Walter Onnoghen a kotun da’ar ma’aikata da ke Abuja.

Duk da yake babban alkalin bai gurfana da kansa ba lokacin da ake ci gaba da shari’ar ta yau.

ADVERTISEMENT

Rahotanni na bayyana cewa, laifuka shida ake tuhumar Walter Onnoghen, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka, wanda hakan ya saba wa dokar tabbatar da da’a ta Code of Conduct Bureau kamar yadda gwamnatin tarayya ta zarginsa da aikata wa.

ADVERTISEMENT