✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara zaman sulhu tsakanin Olubadan da hakimansa 

Manyan hakimai 21 da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Alhaji Abiola Ajimobi ya daukaka  matsayinsu zuwa sarkuna a masarautar Ibadan sun yi zaman sulhu da Olubadan…

Manyan hakimai 21 da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Alhaji Abiola Ajimobi ya daukaka  matsayinsu zuwa sarkuna a masarautar Ibadan sun yi zaman sulhu da Olubadan na Ibadan a ranar Litinin da ta gabata inda suka tattauna a kan takaddamar da ta haifar rabuwarsu da zuwa kotu domin warware matsalar. Takaddama a tsakanin Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji da manyan fadawansa da hakimai 21 ta faro ne a watan Agustan shekarar 2017,  lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Sanata  Abiola Ajimobi ya daukaka matsayin hakiman zuwa sarakuna  inda Olubadan ya ki amincewa da haka.

Tun daga wancan lokaci ne aka fara kiran wadannan sababbin sarakuna 21 da ‘Oba’ wato Sarki, inda suka rika sanya hular sarauta tare da kebe kansu daga halartar taron da Olubadan ya saba yi da su a fadarsa da ke Unguwar Popoyemoja a birnin Ibadan suka rika yin nasu taron daban. Hakan ne ya sa fadar Olubadan ta shiga kan daukaka darajar hakiman zuwa sarakuna a Babbar Kotun Ibadan wacce ta yanke hukuncin dakatar da sababbin sarakunan daga ci gaba da kiran kansu sarakuna.

Aminiya ta gano cewa, an ci gaba da takaddama a tsakanin Olubadan da tsohon Gwamna Abiola Ajimobi wanda ya daukaka kara zuwa kotun gaba tare da barazanar sauke Olubadan daga sarauta har zuwa lokacin da sabuwar gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Seyi Makinde, da ya dauki matakin tsame kansa daga shiga cikin takaddamar.

Hakan ne ya sa jagoran sababbin sarakunan, Otun Olubadan Sanata Lekan Balogun, da wadansu daga cikinsu suka ziyarci fadar Olubadan a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi wata tattaunawa da Oba Saliu Adetunji kan yadda za a shawo kan matsalar.

Sababbin sarakunan da suka halarci taron sulhun sai da suka tube hulunan sarauta kafin su shiga fadar Olubadan.

Duk da yake babu wani bayani kan sakamakon taron na minti 40 sai dai Olubadan ya bayyana wa ’yan jarida farin cikinsa da mika godiya ga manyan fadawan nasa kan kokarin yin sulhu domin tafiya tare don ci gaban masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 da Jihar Oyo da kasa baki daya.

Otun Olubadan Sanata Lekan Balogun ya ce, “Mun zo fadar Olubadan ne domin tabbatar da cikakken matsayinta domin bai kamata mu ci gaba da zama irin wannan ba. Muna son cikakken hadin kai domin ci gaban masarautar Ibadan.” Tsohon Gwamnan Jihar, Osi Olubadan Sanata Rasheed Ladoja wanda ke goyon bayan Olubadan kan kin yarda da daukaka darajar hakiman yana cikin manyan fadawa da suka halarci taron.