✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da Jadawalin Kwallon Afirka na CHAN 2020

An fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka na ’yan wasan da ke taka-leda a gida ta bana (CHAN 2020,) inda mai masaukin baki,…

An fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka na ’yan wasan da ke taka-leda a gida ta bana (CHAN 2020,) inda mai masaukin baki, Kamaru, za ta fafata da Zimbabwe a bikin bude gasar ranar 4 ga Afrilu mai zuwa.

Sashin Hausa na Rediyon BBC ya ce, Indomitable Lions za ta fafata da Zimbabwe ne a filin wasa na Ahmadou Ahidjo, wanda a nan ne za a buga karawar karshe ranar 25 ga watan Afrilu.

Mai rike da kofin kasar Moroko za ta fara karawa ce da Togo ranar 6 ga Afrilu, kafin ta fafata da Rwanda da Uganda a rukuni na uku.

Gasar ta CHAN da za a yi wadda ta kunshi ’yan wasa da ke taka-leda a gida ta sa an sauya lokacin kare gasar Zakarun Afirka ta Champions League da ta Confederation Cup zuwa wata biyu.