✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da sunayen ’yan kwallon da za su fafata a gasar zakaran dan kwallon duniya

Shahararren dan kwallon kafar Real Madrid da yanzu haka ya fi kowane dan kwallo tsada a duniya, yana daga cikin ’yan kwallo guda 23 da…

Shahararren dan kwallon kafar Real Madrid da yanzu haka ya fi kowane dan kwallo tsada a duniya, yana daga cikin ’yan kwallo guda 23 da Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar a ranar Talatar da ta wuce da ake sa ran za su fafata a gasar neman zakaran dan kwallon kafa na duniya na bana.
Gasar, wacce kococi (masu horarwa) da kyaftin-kyaftin da kuma ’yan jarida na kasashen duniya ne ake sa ran za su kada kuri’a don zabo gwarzon dan kwallon duniya wanda za a yi a ranar 13 ga watan Janairun 2014.
Shi dai Gareth Bale ya canza sheka zuwa kulob din Madrid na Sifen ne daga kulob din Tottenham na Ingila a kan Yuro miliyan 100 kwatankwacin Fam miliyan 85 da dubu 300 bayan ya zura kwallaye 26 a kakar wasan da ta ta wuce a kulob din Tottenham.
Sauran ’yan kwallon da za su fafata don neman lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sun hada da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Edison Cabani da Radamel Falcao da Eden Hazard da Zlatan Ibrahimobic da Andre Iniesta da Philip Lahm da Robert Lewandowski da Thomas Muller da Manuel Neur da Neymar da Mesut Ozil da Andrea Pirlo da Franck Ribery da kuma Arjen Robben.
Sauran su ne Bastian Schweinsteiger da Luis Suarez da Thiago Silba da Yaya Toure da Robin ban Persie da kuma dabi Hernendez.
Lionel Messi ne ya kafa tarihin wanda ya lashe kyautar har sau hudu a jere, don haka idan aka sake zabar sa a wannan karo, zai lashe ta biyar kenan.