✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano dan uwan Kim Jong Un da aka kashe a 2017, dan leken asirin CIA ne

Kim Jong Nam, wanda dan uwan Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, da aka kashe a kasar Malaysia a shekarar 2017, ya kasance…

Kim Jong Nam, wanda dan uwan Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, da aka kashe a kasar Malaysia a shekarar 2017, ya kasance dan leken asirin Hukumar Leken Asirin Amurka (CIA) ne, kamar dai yadda jaridar World Street Journal ta ruwaito.

Jaridar ta ruwaito wani mutum da ba ta ambaci sunansa ba, wanda ta ce yake da masaniya game da batun, ta kuma bayyana cewa babu wani karin haske kan dangatar Kim Jong Nam da CIA.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters bai tabbatar da sahihancin labarin ba. Ita kuwa hukumar CIA ta ki cewa uffan game da rahoton.

Jaridar da ambato mutumin ya na mai cewa: “Da akwai dangantaka mai karfi” tsakanin hukumar ta CIA da Kim Jong Nam.

“Tsoffin jami’an Amurka da dama, sun ce dan uwan Shugaban kasar, wanda yayi shekaru da dama na rayuwarsa, ba a san shi da wani iko a birnin Pyongyang ba, dan haka ba mai yiwuwa bane a ce yana da wasu bayanan asirin kasar da zai kwarmata wa CIA ba,” inji jaridar.

Jaridar ta kuma ci gaba da cewa, tsoffin jami’an sun ce Kim Jong Nam, kusan akwai tabbacin cewa yana tuntubar hukumomin leken asirin wasu kasashen, musamman ma China.

Jami’an gwamnatocin Koriya ta Kudu da kuma na Amurka sun ce, hukumomin Koriya ta Arewar ne suka bayar da umurnin a kashe Kim Jong Nam, wanda ya kasance mai matukar suka kan mulkin iyalan gidansu. Sai dai mahukuntan birnin Pyongyang sun musanta zargin.

An gurfanar da wasu mata biyu gaban kotu bisa tuhumar watsa wa Kim Jong Nam gubar BD na ruwa da aka haramta a fuska, a tashar jiragen saman birnin Kuala Lumpur, cikin watan Fabrairun 2017. Sai dai mahukuntan Malaysian sun saki Doan Thi Huong, ‘yar kasar Bietnam, a watan Mayu da kuma ‘yar kasar Indonesia Siti Aisyah a watan Maris.

Kamar dai yadda Jaridar ta World Street Journal ta ruwaito, mutumin da ya tsegunta ma ta bayanan sirrin, ya ce Kim Jong Nam ya tafi zuwa kasar Malaysia a Fabrairun 2017 da nufin ya gana da jami’an CIAn, koda yake, wannan kadai ba zai zama makasudin ziyarar tasa ba.