✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawa a haramtacciyar rijiyar man fetur

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Sibil Difens (NSCDC) ta gano gawar wani mutum mai shekara 45 a cikin wata haramtaciyar rijiyar man fetur a…

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Sibil Difens (NSCDC) ta gano gawar wani mutum mai shekara 45 a cikin wata haramtaciyar rijiyar man fetur a yankin Ogijo a Jihar Ogun.

Mai magana da yawun hukumar na Jihar Ogun, Dyke Ogbonnaya ya bayanna cewa gawar da aka gano ta wani mutum ne dan asalin jihar Oyo mai suna Musa Oladipupo wanda daya ne daga cikin masu ta’asar fasa bututun man fetur na babban kamfanin mai na kasa na NNPC dake yankin.

“Jami’an hukumarmu ta NSCDC sun gano gawar ne a cikin wata haramtaciyyar rijiyar mai da masu fasa bututun mai ke amfani da ita a yankin na Ogijo, ya ce an samu gangarwar jankar mai lita 30 a tare da gawar, wanda mutumin ya yi yunkurin dibar man da ita. Don haka zamu ci gaba da zage damtse wajen hana ayyukan masu fasa bututun man fetur a yankin baki daya,” a cewarsa.