Da Dumi Dumi

An gano gawar malamin jami’ar Ondo da aka yi garkuwa da shi

A karshen makon jiya ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace malamin jami’ar jihar Ondo Farfesa Gideon Okedawo.

Malami a tsangayar lissafi na jami’ar kuma Shugaban kungiyar manyan ma’aikatan makarantar ta SSANU Temidayo Temola, ne ya sanarwa manema labarai hakan a safiyar yau Talata cewa, malamin jami’ar ya mutu a hannun masu garkuwa da shi inda aka gano gawar tasa.

An yi garkuwa da marigayin a kan hanyar Auchi a jihar Ondo a karshen makon jiya inda jami’an ‘yan sanda suka gano motarsa a gefen hanya bayan an yi garkuwa da shi.

Share