✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawarwaki 30 da aka birne a Benuwe

‘Yan sandan jihar Benuwe, sun ce sun gano wasu boyayyun gawarwaki 30 da aka birne a makabartar kauyen Gbatse, wanda ake zargin wasu miyagun mutane…

‘Yan sandan jihar Benuwe, sun ce sun gano wasu boyayyun gawarwaki 30 da aka birne a makabartar kauyen Gbatse, wanda ake zargin wasu miyagun mutane ne suka kashe a garin da ke Karamar Hukumar Ushongo. Majiyarmu ta gano cewa an gano gawarwakin ne a yankin wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a yankin.

Wasu mazauna unguwar da aka samu gawarwakin sun ce, sun dade su na samun yawan bacewar ‘yan uwan su, a cikin wadannan gawarwakin da aka gano suka samu wadanda suka bace.

Jami’ar Hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar ASP Catherine Anene, ce ta sanar da hakan a wata tattaunawa da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) yau Alhamis a Makurdi babban birnin Jihar.

ASP Catherine, ta ce a yanzu haka an kama mutum daya da ake zargi da kisan mutanen, kuma da zarar an kammala bincike za a sanar da cikakken rahoton.