✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gidajen kogo a Libiya

A tsaunukan Yammacin Nafusa da ke garin Gharyan, a samu gidaje masu zurfin mita 10 a karkashin kasa, inda wani mazaunin gidajen, Arabi Belhaj ke…

 Belhaj yana hada shayi a cikin gidansa na kogon karkashin kasaA tsaunukan Yammacin Nafusa da ke garin Gharyan, a samu gidaje masu zurfin mita 10 a karkashin kasa, inda wani mazaunin gidajen, Arabi Belhaj ke hada shayi, ya zauna a kan darduma mai launuka, inda ya ajiye tukunyar shayinsa a kasa. Wannan mutum dan shekara 43, wanda ya siffanta kansa a matsayin mutumin da.
dakin Belhaji an kawata shi da dardumai na alfarma masu launuka da alkuki da tukwane. Kuma kowane gida mai tsawon mita 10, an raba shi zuwa sashi uku, inda iyaye ke kwana a wani bangare da dakin yara, da kuma babban dakin hutawa. An yi kofa da itacen zaitun. Gidan yana da dumi a lokacin sanyi; sannan yanayin sanyi a lokacin zafi.
“Irin wadannan gidajen babu kowa a cikinsu, domin mafi yawancin iyalan da ke zaune a cikinsu, sun fice daga gidajen tun a shekarar 1985,” a cewar dan uwan Belhaj, mai suna Abdulrahaman.
wadannan gidajen kogo sun bayyana a cikin tsaunukan Yammacin garin Gharyan da ke da nisan kilomita 100 a Kudancin Tripoli. Arabi Belhaj yan hada shayi a cikin gidan kogonsa.