Da Dumi Dumi

An gano karen da ya yi shekara dubu 18 bayan mutuwarsa

Karen da ya yi shekara dubu 18 bayan mutuwarsa mai suna Dogor
Karen da ya yi shekara dubu 18 bayan mutuwarsa mai suna Dogor

Bayan gwajin wani jinsin dan kare da aka yi ta hanyar kwayar halittarsa a wani wajen danshi a cikin lardin Siberia da ke kasar Rasha, an gano cewa bai da asalin jinsin halittar irin karnukan wannan zamanin.

Abin mamakin shi ne yadda aka adana karen da ya yi shekaru dubu 18 bayan mutuwarsa a garin Siberia, sai dai har yanzu masu binciken kimiyya na ci gaba da tantance gano shin karen gida ne ko na dawa?

A yanzu haka an rada wa karen suna ‘Dogor’, ma’ana aboki a harshen kabilar garin. An dai samu wannan karen ne a kusa da Unguwar Yakutsk a Siberiya ta Gabas lokacin hunturun da ya gabata.

An gano karen jinsin namji ne, yayin da hancinsa da hakoransa da fatar jikinsa na cikin yanayi mai kyau.

Wani mai bincike na musamman mai suna Lobe Dalen, ya ce “Wannan shi ne tsohon karen da aka taba samu mai wannan shekarun ke nan a tarihi” wanda aka adana.

ADVERTISEMENT

Wannan karen yana kama da wanda kamar yanzu ya mutu.

An gano adadin shekarun karen ta hanyar gwajin kashin kirjinsa.

Wani mai bincike a cibiyar biciken abubuwan tarihi mai suna Dabid Stanton, a kasar Sweden, ya ce abu ne mai sauki a iya tantance karen gida da na daji.

Dabid ya bayyana wa kafar sadarwa ta CNN cewa, suna da kwararrun alamomi da za a iya tantance wane irin jinsin kare ne.

“Ba za mu iya saurin tantancewa ta hanyar yawan adadin karnukan gida da na daji ba.”

Dabid yana kyautata zaton cewa, Dogor jinsi biyu yake da shi, na gida da na dawa.

Mujallar Nature Communications a shekarar 2017, ta wallafa cewa jinsin irin wannan karen ya yi rayuwarsa kimanin shekaru dubu 20 zuwa dubu 40 da suka gabata.

A nazarin da Jami’ar Odford ta yi, wanda aka wallafa a mujallar kimiyya  na cewa, karen yana da irin wannan jinsin wanda ya bayyana a Nahiyar Turai da Asiya

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya