Daily Trust Aminiya - An gano mai ciki wata 8 cikin maniyyatan Jigawa
Subscribe

An gano mai ciki wata 8 cikin maniyyatan Jigawa

Jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa sun gano wata mata mai dauke da cikin wata takwas bayan ta tsallake duk binciken jami’an tantance maniyyata suke yi, inda take kokarin hawa jirgi dauke da jakar guzurinta, kafin wani jami’in hukumar ya gano tanada ciki, sannan aka dakatar da ita.

Shugaban Hukumar, Malam Sani Alhassan ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya sakaya sunan matar da sunan karamar hukumar da ta fito.

Ya ce maniyyata 893 ne jirgin na Mad Air ya dauka zuwa kasar Saudiyya daga filin jirgin da ke Dutse, kuma ana sa ran za a sauke su ne kai-tsaye a Birnin Madina.

Ya kara da cewa mahajjatan jihar sun hada da ma’aikatan Hukumar  Hajji ta Kasa da na hukumarsu da jami’an tsaro da malamai masu fadakarwa.

A lokacin hada wannan labarin, saura ragowar maniyyata daga kananan hukumomi tara suka rage daga jihar.

texem
More Stories