✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano masana’antar jarirai a Anambra

Sashen kula da hana safarar yara a karkashin Hukumar Yaki da Safarar Mutane da Cin Zarafin Yara (NAPTIP) ya ce ya gano wasu gidaje biyu…

Sashen kula da hana safarar yara a karkashin Hukumar Yaki da Safarar Mutane da Cin Zarafin Yara (NAPTIP) ya ce ya gano wasu gidaje biyu a kauyen Obosi da ke Karamar Hukumar Idemili ta Arewa  a Jihar Anambra inda ake kyankyasar jarirai bayan an ajiye yara mata suna rainon juna biyu har su haihu a biya su kudi a karbe jariran.

Asirin gidajen ya tonu ne kamar yadda wakilin Aminiya ya ruwaito a wani samame da jami’an hukumar suka kai kan gidan. Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar,  Ndidi Mezue ce ta sanar da haka, inda ta ce an gano wadansu yara ’yan mata biyu  daga cikinsu dauke da tsohon ciki ba su da koshin lafiya, ganin haka jami’an hukumar suka kubutar da ’yan matan biyu suka kama manajan gidan daga nan hukumar ta ci gaba da farautar irin wadannan gidaje da ake ajiye ’yan mata ana kyankyasar  jarirai da su.

Gida na biyu an bude shi  ne da sunan gidan marayu amma hukumar ta gano jarirai ake sayarwa.

Wata majiya da ke kusa da gidan da ake kyankyasar jariran da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa gidan ana tara mata ne da suka samu juna biyu kuma ba su son su iyayensu su gane, idan suka haihu sai a karbe abin da suka haifa a sallame su da kudi kadan.

Hakar kyankyasar jarirai ana sayarwa harka ce da ta kankama a Kudu maso Kudu, inda mutanen yankin ke gani hanya ce ta samun kudi cikin sauki.

Ayarin jami’an tsaro da suka kai samamen sun hada da ’yan sanda da  jami’an tsaro na sirri da kuma jami’an tsaro na sibil difens kaya da jami’an Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar inda suka ziyarci garuruwan Ogidi da Nkpor da kuma Anacha.