✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano motoci biyar da aka sace a Benuwe

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwe Ene Okon ya ce, an gano motoci biyar da aka sace. Okon ya ce, kusan wata daya kenan da sace…

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwe Ene Okon ya ce, an gano motoci biyar da aka sace.

Okon ya ce, kusan wata daya kenan da sace motocin, ‘yan sandan dai sun yi amfani da hikima wajen bankado wadanda ake zargin cewa sun shahara wajen sace motocin jama’a daga wajen da suke ajiye wa, musamman a Makurdi babban birnin jihar da kewayen jihar.

A cikin makonni biyu kadai an gano motoci biyar da aka sace, daya daga cikin motar ta tsohon Kwamishinan ‘yan sanda ce.