✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano mutum 150 da ke karbar fansho da albashi a Borno

A makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya kafa wani kwamitin mutum bakwai wanda zai kara zakulo tare da duba…

A makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya kafa wani kwamitin mutum bakwai wanda zai kara zakulo tare da duba sha’anin biyan fansho a jihar, kasancewar a baya kwamitin tantance ma’aikata ya gano wasu ‘yan fanshon da ke karbar albashi kuma su karbi fansho su 150.

Haka kuma kwamitin ya gano rarar sama da Naira Miliyan Dubu 8, abin da ya haifar da tsaiko a wajen biyan fanshon har ta kai ga ‘’yan fanshon gudanar da zanga-zangar lumana da nufin tunawa gwamnati ta biyasu hakkinsu.

Malam Muhammadu Babale, yana daya daga cikin ‘yan fanshon da gwamnati ya kira don yi masu bayanin halin da ake ciki, ya ce “a gaskiya mun gode wa Allah da muka zo muka sami wannan bayani dalla-dalla, wanda ada bamu san halin da ake ciki ba, to amma zuwan ya bamu damar sanin halin da ake ciki, wanda shine ma ya haifar da tsaikon rashin biyanmu hakkinmu. Kuma abin bakin ciki ne kwarai ace mutum yana karbar fansho kuma ya zagaya ya je ya karbi albashi.”

“Don haka muna goyon bayan yin bincike tare da hukunta duk wadanda aka samu da laifi, amma kuma a waje daya ina rokon gwamna da ya yi wa Allah ya taimaka mana ya biya mana hakkokinmu a kan lokaci, kada wancan laifin ya shafe mu, domin muna cikin halin damuwa na kasancewar duk harkokinmu da iyalanmu sun tsaya cik, an dakatar da ’ya’yanmu a makarantu saboda rashin biyan kudin makaranta,” a cewarsa.