✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano yarinyar da fasto ya sace bayan shekara 7

Kungiyar  Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Kaduna, ta dawo da wata yarinya ’yar shekara 12 gida wadda ake zargi wani limamin coci ya sace…

Kungiyar  Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Kaduna, ta dawo da wata yarinya ’yar shekara 12 gida wadda ake zargi wani limamin coci ya sace ta ya kai ta Jos, Jihar Filato shekara bakwai da suka wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa, an sanar da bacewar yarinyar mai suna Sadiya ne tun a shekarar 2013, bayan iyayenta sun yi kokarin neman ta amma abin ya ci tura, duk da sun sanar a kafafen yada labarai da kuma masallatai.

Sakataren JNI Malam Ibrahim Kufaina ya shaida wa manema labarai cewa faston ne ya dauke Sadiya ya yi mata rajista a makarantar mishan ba tare da amincewar iyayenta ba.

Ya zargi limamin cocin da yin garkuwa da budurwar, sauya mata addini, hana ta hulda da iyayenta da ’yan uwanta da addininta kuma ba tare da an san halin da take ciki ba.

Kazalika, kungiyar ta zargi faston da cin zarafin budurwar a tsawon shekarun da ta shafe ba a hannun iyayenta ba.

A cewar Sakataren na JNI, “Shekara bakwai da suka wuce aka sanar da bacewar yarinyar, sai aka samu rahoton cewa, ta hadu da wani mutum a cikin gonarsa, sannan ta bayyana masa cewa tana son ta sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci, shi kuma ya kai ta wajen fasto a unguwar Barakallahu.

“Faston ya sanya ta makarantar koyon Kiristancin ne a Jos babban birnin Jihar Filato.

“Idan har limamin Kirista ne mai gaskiya ya kamata ya yi bincike game da yarinyar kafin sauya addininta zuwa Kiristanci.

“A duk  lokacin da Sadiya ta dawo hutu gida, sai faston ya kai ta unguwar Barakallahu lokacin tana shekara 12, a yanzu tana shekara 19.

“Da Allah Ya tona asirin faston, wata rana, da yake ana barin dalibai shiga birane, sai ta hadu da wasu ’yan uwa Musulmi ta fara bayanin halin da ta tsinci kanta.

“Sai suka saya mata wayar salula da sabon layin kiran waya suka sa ta a mota don mai da ita garinsu — zuwa Kaduna”, a cewarsa.

Sakataren ya kara da cewa, sanadiyar bacewar Sadiya zuciyar mahaifinta ta buga wanda hakan ya yi sanadin rasuwarsa.

Ya kara da cewa kakar yarinyar da take rikonta ita ma ta rasu saboda tunanin bacewarta.

Malam Ibrahim ya bukaci Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna da su shiga cikin lamarin.

JNI ta kuma bukaci Kungiyar Mata Musulmi (FOMWAN) da ta dauki mataki sannan ta shigar da kara kotu domin tabbatar da adalci.

A yanzu haka an shigar da kara gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna, kuma ana sa ran za a fara sauraron karar a ranar 16 ga Oktoba 2020.