Aminiya

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano, a yanzu hukumomin gidan sun ce an sami zakin.

A jiya Asabar ne zakin ya kufce daga inda ake tsare da shi a gidan adana namun daji na jihar Kano.

ADVERTISEMENT

Tun da farko hukumomin kula da gidan namun dajin sun ce bai fita daga gidan Zoo din ba.

An toshe dukkanin kofofin gidan Zoo da zakin zai iya fita ya shiga gari.

ADVERTISEMENT

Shugaban gidan adana namun dajin na Kano Saidu Gwadabe Gwarzo wanda ya tabbatar wa majiyar BBC faruwar lamarin ya ce an same shi ne a cikin wani babban keji inda aka ajiye Awaki irin na Kudu.

Sai dai kuma ya ce zakin ya yi barna inda ya shiga ya cinye awakin.

“An yi nasarar kulle kejin kafin a yi kokarin yi masa allurar da za ta gajiyar da shi domin a mayar da shi gidansa.” in ji shi.