✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An girke ’yan sanda dubu 40 don zaben Gwamnan Osun na gobe

Hukumar ’Yan sandan Najeriya ta bayar da umarnin girke jami’an tsaro dubu 40 a karkashin shugabancin wani Na’ibin Sufeto Janar da Mataimakan Sufeto Janar 2…

Hukumar ’Yan sandan Najeriya ta bayar da umarnin girke jami’an tsaro dubu 40 a karkashin shugabancin wani Na’ibin Sufeto Janar da Mataimakan Sufeto Janar 2 da kwamishinonin ’yan sanda 8. Ayayin ’yan sandan zai yi aiki da jiragen helkwafta 2 da motoci masu sulke don tabbatar da tsaro a lokacin zaben Gwamnan Jihar Osun da za a gudanara gobe Asabar.

Mataimakin Sufeto Janar mai kula da shiyya ta 11 da ke Osogbo Malam danjuma Ibrahim, ya shaida wa Gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi lokacin da ya ziyarce shi a Ibadan  cewa yanzu hukumar ’yan sandan ta girke jami’an tsaro dubu 40 don sanya ido wajen tabbarar da ganin an gudanar da zaben na gobe a Jihar Osun lami lafiya. Ya ce, an umurci jami’an tsaro su sanya ido sosai musamman a kan hanyoyin shiga cikin Jihar Osun domin dakile miyagun mutane da ke son tayar da zaune-tsaye a lokacin zaben.

Ya ce wannan ziyara ce ta musamman da ya kawo Jihar Oyo, domin rokon Gwamna Ajimobi ya taimaka wajen wayar da kan jama’ar jihar game da muhimmancin kaurace wa miyagun ’yan siyasa da suke son yin hayarsu, domin tayar da hargitsi a wuraren kada kuri’a a zaben na gobe. Kuma ya roki Gwamnan ya taimaka wa jami’an wajen gyara motocin kwantar da tarzoma da suka lalace.

“Ba mu bukatar samun matsala ko kadan, musamman saboda mun lura cewa akwai wadansu mutane da suke yunkurin tashi daga Jihar Oyo zuwa Jihar Osun domin tayar da rikici. A dalilin haka na sanar da Kwamandan Runduna ta 2 ta Sojojin Najeriya da dukan kwamishinonin ’yan sandan da suke shiyya ta 11 don su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin ganin sun gudanar da ayyukan tsaro lami lafiya a lokacin zaben,” inji shi.

Sassa daban-daban na ’yan sanda da suka samu horo a kan al’amarin zabe ne za su gudanar da ayyukan tsaro a rumfunan zabe 3,764 a cikin mazabu 332 na kananan hukumomi 30 domin tabbatar da an gudanar da zaben lafiya.