Search
Subscribe
An gudaanr da taron KILAF 2019 a Kano

Kyautar Gwarzon Darakta da aka ba Darakta Yaseen Auwal

An gudaanr da taron KILAF 2019 a Kano

A makon jiya ne aka gudanar da taron baje kolin fina-finai da kuma karrama ’yan fim na Afirka mai taken Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festibal (KILAF 2019) da aka gudanar karo na biyu a birnin Kano

Taron wanda aka shafe mako guda ana gudanarwa an bude shi da gabatar da jawabai kan yadda sana’ar fim take da yadda za a gudanar da ita musamman a wannan lokaci da ake samun ci gaban zamani da ke neman kashe harkar musamman a masa’antar fina-finai ta Kannywood da yanzu ake ganin kamar ta dauki hanyar durkushewa. Don haka ne ma taron ya mayar da hankali ga lalubo hanyar da za a shawo kan matsalar da harkar take ciki a yanzu.

Da yake jawabin maraba a wajen Shugaban Taron Malam Abdulkarim Muhammad, ya bayyana matukar farin cikinsa game da samun halartar da bakin suka yi inda wadansunsu ma sun zo ne daga nisan duniya domin hlartar taron inda ya yi fatar samun nasarar taron.

An ci gaba da taron da yin bita a kan sanin makamar aiki inda aka kasa taron gida biyu  da karamin aji da babba,  kuma ’yan fim da dama suka halarta kamar su Ishak Sidi Ishak da  sauransu.

A rana ta gaba an gudanar da taron cin abinci tare da gabatar da sunayen fina-finan da suka tsallake matakin tantancewa, inda aka gabatar da fina-finai 3 da suka tsallake matakin tantancewa cikin fina-finai da dama da suka shigar gasar.

A rana ta karshe an kammala taron da raba kyaututtuka ga jarumai da fina-finan da suka ci gasar ta KILAF AWARD

Fim din Khul’i ne ya lashe kyautar gwarzon fim, sannan fim din ya zama mafi kyan labari wanda Ahmad Alkanawi ya rubuta. Haka nan Yaseen Auwal ya zamo Gwarzon Darakta da fim din Fuska Biyu  sai fim din Kumbar Susa wanda ya fi kowane fim daukar hoton bidiyo.

Gwarzon Jarumi na gasar Kilaf Award 2019 shi ne Ibrahim Mandawari, sai Gwarzuwar Jaruma Rahma Hassan da fim din Sandar Kiwo. Sai fim din da ya yi nasara da mafi tsara kwalliya da kuma gajeren fim din da ya samu kyauta shi ne fim din Dan Kasa.

Shugaban taron ya kara da cewa duk da cewa an samu ci gaba a taron na bana kasancewar daga ’yan fim din Hausa sun halarci taron amma har yanzu akwai sauran kalubale na karbar sabon yanayin da taron ya zo da shi a tsakankanin ’yan fim din. “Alhamdulillah a bana an samu ci gaba fiye da bara. Sai dai na san cewa abu na gyara dama sai a hanlkali yake samun karbuwa. Saboda haka muna sa rai nan gaba ’yan fim da dama za su shigo cikin wannan harka a yi tare da su, domin abin na su ne,” inji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin