✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gudanar da bikin Wanzamai a masarautar Gombe

A ranar asabar din da ta gabata ne Jihar Gombe ta cika da bakin sarakunan Aska na jihohin Arewacin Najeriya da wasu sassan kasar har…

A ranar asabar din da ta gabata ne Jihar Gombe ta cika da bakin sarakunan Aska na jihohin Arewacin Najeriya da wasu sassan kasar har da Nijar domin gudanar da wasan wanzamai.

Da yake jawabi a wajen bikin wasan wanzaman, Sarkin Askar Jihar Gombe Alhaji Sani Sambo, ya nuna jin dadinsa da godiya ga daukacin Wanzamansu na Jihar Gombe na yadda suka ba da hadin kai da goyon baya domin ganin wasan ya gudana  lafiya da jin dadi.

Sarkin Askar Gombe, ya kuma ce sun dade suna jiran zuwan wannan rana da za su gudanar da wannan wasan na gado Allah bai yi ba sai yanzu kuma, sannan kuma ya nuna farin cikinsa a kan yadda wasan ya kayatar da ’yan kallo.

Ya ce taro ne wanda aka jima ba a yi shi ba a Gombe sai yanzu da suka yi zama suka hada kai don magance duk wata baraka da ke tsakaninsu, wanda a dalilin wannan haduwa tasu ne ya nuna wa duniya cewa kansu a hade yake babu baraka tsakaninsu.

Har ila yau, ya sake yin kira ga dukan wanzamansu da su hada kai don tafiyar da ayyukansu  na wanzanci gaba ba a nan Gombe kadai ba ma, a duk fadin Najeriya da ma Afirka ko duniya baki daya.

Da yake nasa jawabin a wajen taron, shugaban Majalisar Sarakuann Askar Najeriya wanda kuma shi ne Sarkin Askar Jihar Kano Dakta Muhammad Yunusa Nagogo, kira ya yi ga gwamnatin Gombe da cewa yana da kyau ta ja Wanzamai da Sarakunan Aska a jikinta.

Dakta Muhammad Yunusa Nagogo, ya ce yana cike da farin ciki kan yadda wannan taro na wanzamai ya gudana sai dai ya ce su a Kano gwamnati tana yi da su shi ya sa yake kira ga Gwamnatin Gombe da ta ja su a jiki saboda muhimmancin su.

Shi kuwa Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda Mai ba shi shawara kan harkar tsaro Kanal Magaji Kuji Pilam mai ritaya, ya wakilta cewa ya yi daga wannan lokaci gwamnati na tare da kungiyar wanzaman kuma za ta ci gaba da damawa da su a duk wani abu da ya taso.

Gwamna Dankwambo, ya ce bai san haka sana’ar wanzancin take ba, ya dauka sana’a ce kawai da wanzami zai ma aski ka biya kawai ya tafi, sai ya lura ashe suna taka rawar gani wajen bada magunguna da kiwon lafiya sannan kuma gashi har Doktoci da Lauyoyi suke da su a kungiyar.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar kiwon lafiya ta Jihar Gombe Dokta Ishaya Kennedy, Wanda ya samu wakilcin Mista Moses K. Sambo, ya bayyana cewa sana’ar wanzanci sana’a ce mai dadaddiyar tarihi kuma mai daraja.

Sai ya yi kira ga Wanzaman da cewa su dinga tsabtace kayayyakin aikinsu da zai sa ba za a raina musu ba.

Kwamishinan ya ce sana’ar wanzanci dadaddiyar sana’a ce amma dai ana kira da a inganta ta a kuma  a rika tsabtace kayayyakin aikinsu don gudun kamuwa da wasu cututtuka.

Taron ya samu wakilcin sarakunan Askar daga sassan Najeriya da ma kasar Nijar, kuma a lokacin taron wanzamai da dama sun nuna wasan gado iri iri, inda  har wani wanzami daga Jihar Taraba ya hadiye kwan kaza ya fitar da kaza a filin.

Dokta Aminu Abdullahi  Sarkin Askar Potiskum, shi ma ya burge ’yan kallo sannan wanzamai da dama sun nuna bajintarsu ta gado a wajen wasan.