✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gudanar da taron kafa gidauniyar Shata a Kaduna

A ranar Asabar 15 ga watan Yuni, 2013 da misalin karfe 11:00 na safe aka gudanar da taron kafa gidauniyar tunawa da marigayi Mamman Shata…

A ranar Asabar 15 ga watan Yuni, 2013 da misalin karfe 11:00 na safe aka gudanar da taron kafa gidauniyar tunawa da marigayi Mamman Shata a gidan Sardauna da ke unguwar Sarkin Musulmi a Kaduna.
Shugaban taro Malam Kabir Umar ne ya yi jawabin maraba, sannan ya yaba wa wanda ya nemi a kafa gidauniyar.
A lokacin da Editan jaridar Blueprint Ibrahim Sheme yake jawabi, wanda shi ya nemi a kafa gidauniyar ya ce: “Wannan rana ce da muka yi zaman farko don yunkurin karrama Alhaji (Dk.) Mamman Shata Katsina, wannan karramawa ita ce ta farko da aka yi masa tun bayan rasuwarsa a ranar 18 ga Yuni, 1999.”
“Mun ga dacewar a kafa wata gidauniya don tunawa da shi, wadda za ta rika aiwatar da wasu tsare-tsare da ayyuka wadanda za su sa a ci gaba da tunawa da shi.”
Gidauniyar za ta rika shirya taro na kwana daya duk shekara, inda za a kira masana su gabatar da jawabi a kan Shata da ayyukansa, sannan a yi masa addu’a. Wannan taro za a rika shirya shi a daidai ranar da ya rasu, wato 18 ga watan Yuni. Masoyan Shata da iyalansa da jami’an gwamnati za su iya halartar taron. Idan abin ya bunkasa, za a iya mayar da taron na kwana biyu ko na mako daya, inda za a yi kamar kalankuwa ta makada da mawakan Hausa.
Gidauniyar  za ta iya yin jagora wajen kafa wata cibiya, misali, Cibiyar Mamman Shata (Mamman Shata Centre) ko Cibiyar Mawakan Hausa Ta Mamman Shata (Mamman Shata Hausa Music Centre). Cibiyar za ta kasance wani gidan tarihi da za a tara duk wasu abubuwan tarihi da suka shafi Shata. Za a tattaro duk wakokinsa a adana su don a samar da su ga masu bincike da kuma saurare.
Mamuda Mamman Shata, dan marigayin ya roki alfarmar idan za a kafa cibiyar to a kafa ta garin Funtuwa, inda ya yi alkawarin bayar da wadansu kayayyakin tarihi da ya gada daga mahaifinsa.
A karshe an zabi shugabannin riko. Ga yadda aka yi zaben: Hamisu Adamu (Shugaba) daga Funtuwa, Ibrahim Sheme (Sakatare) daga Kaduna, Yusuf Tijjani (Sakataren Kudi) daga Kano, Barista Jamila Mamman Shata (Mai ba da shawara kan shari’a) daga Abuja, sai Kabir Umar (Jami’in hulda da jama’a) daga Katsina.
An rufe taron da misalin karfe 3:30 na yamma.