Da Dumi Dumi

An guntule hannun magidanci wajen murnar nasarar Tambuwal

Abdullahi Shehu wanda aka guntuke wa hannu a Sakkwato
Abdullahi Shehu wanda aka guntuke wa hannu a Sakkwato

Wani magidanci ya rasa hannunsa lokacin da yake zagayen nuna murnar lashe zaben Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal bayan da wadansu mutane suka sare tare da guntulen hannunsa.

Magidanci mai shekara 41 mai suna Abdullahi Shehu wanda yake da mace daya da ’ya’ya hudu yana zaune ne a Unguwar Kofar Kade a birnin Sakkwato.

Abdullahi Shehu ya hau kan babur dinsa ne yana zagaya gari don nuna murnar lashe zaben da Gwamna Tambuwal ya yi, inda ya rika daga hannunsa daya sama tare da watsa yatsu hudu hudu yana nuna alamar Tambuwal zai sake maimaita shekara hudu, kuma yana isa Unguwar Iraki kusa ga Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi, sai wadansu matasa da aka zargin magoya bayan Jam’iyyar APC ne da suke gefen hanya suka guntule masa hannu.

“Kawai karar mutum muka ji, koda muka zo wurin sai ga hannunsa kasa an guntule,” wani matashi da ke Unguwar Iraki ya shaida wa Aminiya.

Wani matashin ya shaida wa wakilinmu cewa “Wannan mutum ya zo wurin matasan ne da nufin fashe musu tulu, da ya fashe su ko suka guntule hannunsa da takobi.”

ADVERTISEMENT

Aminiya ta ji ta bakin Abudullahi Shehu wanda aka fi sani da Walfiya inda ya ce “A ranar Lahadi mun yi magana da wani abokina zan zo in dauke shi mu tafi gidan gwamnati zuwa karfe 10 safe, uzuri ya kama ni sai bayan azahar na kira shi na fada masa zan zo mu tafi. Haka na baro gida na biyo hanyar don isa wajensa. Ban san saman hanyar matasan ne a wurin tsaye duk wanda ya wuce su tare shi su yi masa illa ba, na zo daidai Iraki ina kan babur dina ina tafiya a hankali, kawai cikinsu wani ya sare ni da takwabi a wuyana na kara hannuna ya sare ni ya sake sara ta karo na biyu na kara kara hannunna a karo na biyu kawai sai hannun ya guntule ya fadi kasa, ni ma na fadi kasa amma ban fita hayyacina ba matasan suka tsere a wurin.”

Ya ce “Sai na dauko wayata mutanen da ke saman kaina suka kira abokin nawa da za mu je gidan gwamnati yana jirana gidansu, da ya zo ya kira tsohon Kwamishinan Lafiya Dokta Balarabe Kakale ya sanar da shi halin da nake ciki, daga nan ya ce a kawo ni Asibitin Kwararru na Jiha. Bayan ya zo ya ce lamarin ya fi karfin nan a tafi da ni Asibitin Kashi na Wamakko, muna can ne Gwamna ya bayar da umarnin kawo ni Asibitin Abuja a halin yanzu an yi min aiki, hannun da ya guntulen ba zai koma ba don an katse jijiyoyinsa.”

Game da zargin ya je fashe tulun matasan ne lamarin ya auku, ya ce wannan maganar ba gaskiya ba ce, “Wanda ya yi min wannan aika-aika ban san shi ba, ban taba kowace hulda da shi ba, saman hanya nake tafiya suka yi min haka. Gidanmu ne ke Unguwar Kofar Kade ni gidan Igwai nake da gidana da iyalina ina sayar da dabbobi a Kasuwar Kara. Ba abin da ya hada ni da su, Allah ne zai saka min.”

Nasarar da Gwamna Tambuwal ya samu tamkar tsallake rijiya da baya ne, inda ya kada dan takarar Jam’iyyar APC da ratar kuri’a 342.

An bayyana shi wanda ya samu nasara a zaben da kuri’a dubu 512 da 2, inda abokin karawarsa Ahmad Aliyu Sakkwato ya samu kuri’a dubu 511 da 660.

Jam’iyar APC ta yi watsi da sakamakon zaben kamar yadda Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar Alhaji Sambo Bello Danchadi ya shaida wa manema labarai. Ya ce sun yi watsi da sakamakon zaben ne saboda ratar da ke tsakani ba ta kai yawan kuri’un da ba a yi zabe ba kuma hakan ya saba wa dokar zabe.

Bello Danchadi ya ce akwai masu zabe da aka hana wa zabe a wasu rumfuna a kananan hukumomin jihar, kuma za su dauki matakin shari’a don kwato wa Sakkwatawa hakkinsu na zaben da suka yi.

Jagoran APC a Jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga magoya bayansu da su zauna lafiya “Ba za mu zauna ba har sai mun samu nasara, ba mu fadi ba da ikon Allah,” inji shi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya