✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da ma’aikatan AMASCO kan satar bakin mai na Naira miliyan 158

Kotun Majistare mai lamba 29 da ke Nomanslan a Jihar Kano ta bayar da umarnin a tsare wadansu ma’aikatan Kamfanin bakin mai na AMMASCO bisa…

Kotun Majistare mai lamba 29 da ke Nomanslan a Jihar Kano ta bayar da umarnin a tsare wadansu ma’aikatan Kamfanin bakin mai na AMMASCO bisa zarginsu da hadin baki wajen sace bakin mai wanda kimarsa ta kai Naira miliyan 158.

Takardar karar ta bayyana cewa wadanda ake zargi ma’aikatan kamfanin ne da aka ba su amanar dauko bakin mai daga Jihar Legas zuwa Kano sai dai maimaikon su kawo shi kamar yadda aka umarce su sai suka hada baki suka karkatar da man, inda suka kwashe wasu tankuna da ke dauke da man da kimarsa ta kai ta Naira miliyan 158 da dubu 800.

Takardar karar ta ci gaba da cewa “Ma’aikatan kamfanin na AMMASCO da ake zargi da badakalar su 22 sun hada da Nura Muhammad da Isa Musa da Umar Idris da Kabiru Isa da Ayuba Tijjani da Murtala Abubakar da Nura Umar da Haruna Umar da sauransu.” Sai dai wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake yi musu na hadin baki da cin amana da sata, laifuffukan da suka saba wa sashe na 97 da 311 da 286 na Kundin Shari’a na Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Hassan Ahmad Fagge ya bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargin a kurkuku, ya kuma dage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba, don fara sauraren shaidu.