✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da malamar jami’a a kotu kan cin zarafin Shugaban Uganda

Yan sanda a kasar Uganda sun tabbatar da kama wata malamar jami’a wadda ta zazzagi Shugaban Kasar Yoweri Musebeni da mahaifiyarsa a shafin sada zumunta.…

Yan sanda a kasar Uganda sun tabbatar da kama wata malamar jami’a wadda ta zazzagi Shugaban Kasar Yoweri Musebeni da mahaifiyarsa a shafin sada zumunta.

Wani Kakakin ’Yan sanda, Emilian Kayima ya ce ana tsare da malamar jami’ar mai fafutika, Stella Nyanzi.

Mista Kayima ya ce an tuhumi malamar da aikata laifin aibanta  Shugaban Kasar a kafofin sadarwa na zamani.

Nyanzi ta kaddamar da gidauniyar sayen audugar ga ’yan matan da suke makaranta ganin gwamnati ta gaza, bayan rubuce-rubucen da ta ci gaba da yi a shafukan sada zumunta a kan Shugaban Kasar da matarsa inda ta rika kiran Shugaban da matarsa a matsayin sakarkaru

Dokta Nyanzi ta soki Ministar Ilimi ta kasar, wacce ita ce Matar Shugaban Kasar, Janet Musebeni, bayan gwamnati ta kasa cika alkawarin da ta yi ga ’yan mata a kasar na ba su audugar kunzugu domin al’ada. Wanda shirin wata hanya ce ta fadakar da ’yan mata a kasar Uganda da ke nuni irin yadda ake korar ’ya’ya mata a makaranta domin kunyar sun kasa sayen audugar a lokacin da suke jinin al’ada.

A lokacin yakin neman zabe, gwamnati ta yi alkawarin samar da audugar mata kyauta ga yara mata wadanda ba su da karfin sayen audugar. Amma Ministar Ilimi Janet Musebeni ta ce Gwamnati ba ta da kudin sayen audugar a wannan kasafi na kudinta, wannan lamarin ya kara harzuka Nyanzi ta ci gaba da caccakar gwamnatin Uganda da Shugaban Kasar da ke kan mulki tun 1986.