✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da mutumin da ya yi wa ’ya’yansa biyu fyade

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta gurfanar da wani direban bas mai suna Adewale Adeleke, dan kimanin shekaru 35 a kotun gargajiya ta Ikeja kan…

Adewale Adeleke da ake zargi da yi wa ’ya’yansa biyu fyadeRundunar ’yan sandan Jihar Legas ta gurfanar da wani direban bas mai suna Adewale Adeleke, dan kimanin shekaru 35 a kotun gargajiya ta Ikeja kan zargin yi wa ’ya’yansa biyu mata fyade har na tsawon shekaru biyu a unguwar Ikotun.
Asirin Adewale Adeleke ya tonu lokacin da babbar ’yarsa, mai kimanin shekaru 13 mai suna Ester (ba sunanta na asali ba) ta shaida wa makwabtansu cewa mahaifinta yana yi musu fyade ita da kanwarta Yomi (ba sunanta na asali ba).
Nan da nan makwabtansu suka sanar da ’yan sanda, aka kama shi ba tare da bata lokaci ba.
Da ’yan sanda suka tsananta bincike sai suka gano cewa Mista Adewale ya shafe kimanin shekaru biyu yana saduwa da ’ya’yan nasa.
Yaran sun tabbatar wa ’yan sanda cewa mahaifinsu ne ya kawar musu da budurci tun lokacin da ya kwato su daga wurin mahaifiyarsu.
Sun bayyana wa ’yan sanda cewa duk lokacin da ya sadu da su, yakan yi amfani da wani farin kyalle ya goge raunin da ya yi musu a farjinsu.
Yaran sun bayyana cewa tun lokacin da mahaifinsu ya kori mahaifiyarsu yake saduwa da su ba kakkautawa kuma ba ya ba su kudin abinci idan suka ki kwanciya da shi.
Mista Adeleke ya amsa laifinsa a gaban kotu inda ya nemi yaran da mahaifiyarsu da jama’a su yafe masa.
Adeleke, wanda ya dora alhakin laifin da ya aikata a kan shaidan, ya yi alkawarin canja halayensa muddin kotun ta yi masa sassauci.
Alkalin kotun, Mai shari’a M.O. Olatunji ya ba da umarnin a yi wa yaran gwaji don gano ko sun kamu da wata cuta, kuma ya ba da umarnin a tsare Adewale a gidan kaso har zuwa  ranar 2 ga watan gobe yayin da za a ci gaba da sauraron karar.