✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haife ta babu hannuwa amma tana girki da wasu abubuwa

Tana yin rubutu daukar hoto da kuma saka Wata mai suna Amy Brooks da aka haifa babu hannuwa kuma take da wani ciwo da ya…

  • Tana yin rubutu daukar hoto da kuma saka

Wata mai suna Amy Brooks da aka haifa babu hannuwa kuma take da wani ciwo da ya haddasa rashin hannuwanta da zai iya shafar kafafunta, duk da haka ba ta bar nakasa ta raunata zuciyarta ba, inda take iya kokarin girka abinci da rubutu da daukar hoto da kuma yin saka.

Tunda farkon samun cikin Amy mahaifiyarta ta yi yunkurin zubar da juna biyun da take dauke da shi sakamakon magungunan cutar da aka rika ba ta tana sha kafin haihuwa don kauce wa haihuwar Amy ba hannuwa ko kafafu.

Iyayen Amy, sun bukaci ma’aikatan asibitin da aka haifi Amy su ajiye ta a cikin daki sannan su ci gaba da shayar da ita, saboda yanayin halittar da aka haife ta da shi.

Amy, ta yi sa’ar rayuwa bayan watsi da iyayenta suka yi da ita, inda wasu iyalai masu suna Brooks suka ci gaba da daukar nauyinta kamar ’yarsu. Amy ’yar birnin Pittsburgh da ke Amurka wadda take da kafar sadarwar bidiyo a Intanet na YouTube ta bayyana yadda take gudanar da rayuwarta.

A wannan kafar sadarwar Amy mai kimanin shekara 37 duk ta bayyana yadda take gudanar da harkokinta na yau da kullum ba tare da hannuwa ba. Ta ce, “Ya zama dole in gudanar da harkoki kamar wadda ba ta da nakasa ta hanya daban da zan iya yi. A koyaushe likitocin asibitin suna kara min karfin gwiwa wajen gudanar da rayuwata, duk da yake iyayena ba su amince da nakasar da aka haife ni da ita ba.”

“Ba kowane lokaci ne nake son tsayawa gaban kyamara ba ina bayyana yadda nake gudanar da rayuwata duk da halin nakasa na rashin hannuwa da nake da ita amma yana iya zama wata hanya ta kara wa wadansu kwarin gwiwa game da yadda za su yi rayuwa a yanayin da Allah Ya halicce su,” inji ta.

Amy, ta kasance tana gudanar da rayuwarta na tsawon shekaru ita kadai, a yanzu haka tana kokarin koyon tukin mota ce kuma tana ci gaba da inganta kafar sadarwar bidiyonta na YouTube ba tare da tallafin kowa ba. Amy ta kara da cewa, “Ban sani ba ko zan iya kiran kaina mai daukar hoto saboda ina da sha’awar daukar hoto a koyaushe, ina amfani da baki da kumatuna tare da kafadata don yin wasu abubuwa.” Sai dai Amy ta kasance tana samun sakonni a kafafen sada zumunta na zamani da ke kara mata kwarin gwiwa wajen gudanar da harkokinta na yau da gobe.

Tun lokacin da Amy ta wallafa tarihinta a shekarar 2014 sai ta fara gabatar da kasidun kwarin gwiwa. Kamar haka “Ina sha’awar in wallafa tarihina ga jama’a, ba kawai don in burge wadansu ba, sai dai kawai muhimmancinsa ga wadansu jama’a kuma kowa yana da dalilinsa na aikata komai,” inji ta.

Babban ci gaban da Amy ta samu shi ne lokacin da ta fara koyon dinki, “Da farko abin da na yi tunani ba zan iya ba, sai ga shi yanzu na cimma burina, ina iya dinka jakar hannu in sayar ta amfani da kafar sadarwar Facebook.” Duk da yake iyayenta sun yi sanadiyyar ta gudanar da rayuwarta ita kadai sannan ta samu nasarar cika burinta.