Da Dumi Dumi

An halatta auren mace fiye da daya a Amurka

Majalisar Dattaawan Jihar Utah da ke Amurka ta kada kuri’ar halatta auren mace fiye da daya.

A baya dokar jihar ta tanadi daurin shekara biyar a gidan yari ga duk wanda ya auri mace fiye da daya a jihar da mafi yawanci Kiristoci ne mabiya Darikar Mormons.

Amma yanzu mutum zai iya auren mace fiye da daya koda yake za a ci tararsa Dala 750 (kimanin Naira dubu 272 da 605 da kwabo 73). Sai dai ana ganin dokar za ta fuskanci turjiya a Majalisar Wakilai.

Kafar labarai ta BBC ta ruwaito dan majalisar da ya gabatar da kudirin dokar, yana cewa dokar da ke aiki a yanzu ta jefa iyalai a halin kyama tare da haifar da wata al’ada ta cin zarafi.

Wacce ta yi zagi wajen gabatar da kudirin dokar, ’yar Majalisar Dattawan Jihar, Sanata Deirdre Henderson, ta cea manufar dokar ba wai Tana nufin a halatta auren mace fiye da daya ba ce kadai, a’a sai dai domin a sassauta hukuncin da ake yi wa masu auren fiye da daya domin su samu sukunin fitowa fili ba tare da tunanin a nuna musu tsangwama ba ko kuma fargabar gurfanar da su a gaban shari’a.

ADVERTISEMENT

“Dokar za ta kuma ba da dama ga masu auren fiye da mace daya su samu saukin cin moriyar muhimman abubuwan more rayuwar jama’a na gwamnati kamar kiwon lafiya da ilimi har ma da damar samun aiki ba tare da wata tsangama ba,” inji ta.

Masu adawa dai na ganin dokar hadari ce musamman ga mata kanana da ake tilasta wa auren masu yawan shekaru.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya