✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hallaka hadimin mataimakin kakakin majalisa yana tsaka da shirin angwancewa

A jihar Ebonyi, wasu ‘yan bindiga sun hallaka daya daga cikin hadiman Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar, Hon. Obasi Odefa daidai lokacin da yake…

A jihar Ebonyi, wasu ‘yan bindiga sun hallaka daya daga cikin hadiman Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar, Hon. Obasi Odefa daidai lokacin da yake shriye-shriyen bikinsa.

Rahotanni sun nuna cewa an hallaka marigayin ne mai suna Kingsley Obasi da daren ranar Laraba lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga aiki.

Daya daga cikin abokan aikin mamacin, Thomas Eluu shine ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na Facebook ya maraicen ranar Laraba.

“Abokin aiki na a Majalisar Dokokin Jihar Ebonyi, Kingsley Obasi, wanda hadimi ne ga Mataimakin Kakakin Majalisar ya rasa ransa sakamakon harbin da ‘yan bindiga suka yi masa har lahira,” inji shi.

Kisan na zuwa ne a daidai lokacin da mamacin ke shirye-shiryen angwancewa sakamakon karatowar bikinsa.

Wata majiya daga iyalan mamacin ta ce ana zargin makasan ‘yan fashi da makami ne sun hallaka shi sannan suka yi awon gaba da jakarsa dake dauke da kudi da kuma katinan gayyatar daurin auren nasa da kuma sauran abubuwa masu muhimmanci.

Majiyar wadda b tai amince a ambaci sunanta ta ya ce harin ya fi kama da na fashi da makami.

“Gaskiya ne an harbe shi, amma ba na tunanin harin na da alaka da siyasa, na fi tunanin kawai na fashi ne,” inji majiyar.