Search
Subscribe
An hallaka jagoran ’yan ta’adda a Mali

An hallaka jagoran ’yan ta’adda a Mali

Rundunar tsaron Faransa ta bayyana kisan daya daga cikin jiga-jigan kungiyoyin jihadi a yayin wani samame da rundunar ta kaddamar a Mali a farkon watan jiya.

Ministar Tsaron Faransa ta tabbatar da kisan Shugaban Kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin a shafinta na Twitter, inda ta ce an hallaka shi ne tun a ranar 9 ga Oktoba. Ali Maychou dai na daya daga cikin shugabannin kungiyoyin addini masu kaifin kishin Musulunci a Mali. Faransa na zargin Ali Maychou ne da hannu wajen kaddamar da hare-haren ta’addanci kan dakarun kasar da na Amurka da na rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin