✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana mai wa’azi shiga Makka saboda goyon bayan Mursi na Masar

An hana mashahurin malami mai wa’azi, dan kasar Kuwait shiga garin Makka don yin Umra a kasar Saudiyya, saboda bambancin ra’ayinsa da kasar a kana…

Tareq Al Suwaidan, malamin da aka hana shiga MakkaAn hana mashahurin malami mai wa’azi, dan kasar Kuwait shiga garin Makka don yin Umra a kasar Saudiyya, saboda bambancin ra’ayinsa da kasar a kana bin da ke aukuw aa kasar Masar. Malamin, Tarek Al Suwaidan ya bayyana a shafin sadarwarsa na twitter cewa:
“an hana ni shiga Saudiyya saboda ra’ayina da matsayina akan juyin mulkin da aka yi a kasar Masar, duk da haka soyayyata ga kasar Saudiyya da al’umamrta ba su sauya ba, kuma ra’ayina na nan bai gushe ba.”
Shehun malamin ya taba fitowa a kafar talabijin, ya bayyana cewa shi dan kungiyar ’Yan uwa Muslimi ne, wato Ikwanul Muslimin, wadda ta shiga zabe, har ta samu nasar dora Shugaba Muhammad Mursi kan karaga. Wannan ra’ayi nasa ya sa aka dakatar da shirin da yake gabatarwa a gidan talabijin din Al Resala dake  kan tauraron dan Adam. Gidan talabijin din mallakar hamshakin mai kudin Saudiyya ne, wato Yarima Al Waleed Bin Talal.
Hamshakin attajiri, Al Waleed Bin Talal, ya rubuta wa shehun malami Tarek Suwaidan wasika, inda ya yi nuni da cewa ’ya’yan kungiyar ’yan uwa Musulmi ba su da muhalli a cikin tasharsa.