✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana tsohon dan damben boding Mike Tyson shiga Ingila

Hukumar shigi da fici ta Ingila ta hana tsohon dan damben boding Mike Tyson shiga Ingila don ya kaddamar da littafinsa.Mike Tyson dai ya shirya…

Hukumar shigi da fici ta Ingila ta hana tsohon dan damben boding Mike Tyson shiga Ingila don ya kaddamar da littafinsa.
Mike Tyson dai ya shirya kaddamar da littafinsa mai suna “Undisputed Truth” ne a wannan mako amma saboda sabuwar dokar kasar da ta nuna duk wanda aka taba zartar masa da hukuncin shekara 4 ko fiye a gidan yari ba za a amince ya shiga kasar ba.
Tyson, dan kimanin shekara 47 an taba samunsa da laifin yi wa wata tsohuwar sauraniyar kyau ta duniya fyade a shekarar 1992 kuma aka zartar masa da hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara shida.  Baya ga haka an sha kama shi da laifin yin mu’amala da kwayoyin koken da yin tuki cikin maye da akuma cin mutuncin mutane babu gaira babu dalili.
Tuni wadanda suka wallafa littafin suka shawarci tsohon dan damben ya canza wurin kaddamar da littafin zuwa birnin Paris da ke Faransa saboda wannan matsala. Mike Tyson tun yana dan shekara 20 ya fara samun nasara a gasar dambe.
Ya yi suna bayan ya gutsure kunnen abokin karawarsa mai suna Ebander Holyfield a wani gasar dambe da suka yi.