Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An haramta fitar da kayan lambu daga Ghana

Hukumomi a Ghana sun dakatar da fitar da kayan lambu da suka hada barkono da yalo sakamakon fargabar da ake yi na suna dauke da kwayoyin cuta ko kuma tsutsa.

Ma’aikatar Noma da Abinci ta kasar Ghana ce ta bayyana cewa dokar haramta fitar da kayayyakin da aka kafa, za kuma ta fara aiki ne daga mako mai zuwa kuma dokar za ta ci gaba har sai abin da hali ya yi.

ADVERTISEMENT

Wannan dakatarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai ta ba kasashen da ke shigar mata da kayayyaki umarnin bayar da rahoto kan yadda suke kula da kwayoyin cuta masu illa ga irin wadannan kayayyakin.

Ita dai Kungiyar Nanoma da kuma masu fitar da kayayyakin lambu ta kasar Ghana ta bukaci gwamnatin kasar ta dage mata wannan dokar, inda ta bayyana cewa dokar za ta jawo matsala ga manoma kusan dubu hudu.

ADVERTISEMENT

Amma hukumomi a kasar sun ki amincewa da haka inda suke tsoron ka da Kungiyar Tarayyar Turan ta kara saka masu takunkumi ganin cewa ba a dade da cire masu takunkumin da aka saka masu kan shigar da kayan lambu ba a bara kamar yadda BBC ya ruwaito.

An rantsar da Peter Mutharika sabon wa’adin mulki a Malawi

An rantsar Shugaban Kasar Malawi Peter Mutharika a sabon wa’adin mulki na biyu bayan ya lashe babban zaben kasar.

Bikin rantsar da shi din ya gudana ne a Babban Birnin Kasuwancin kasar wato Blantyre sa’o’i kalilan bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.

Mista Mutharika, wanda ya fara shugabancin kasar ne a shekarar 2014, bayan ya samu kaso 38.5 cikin 100 na kuri’un da aka samu.

Wanene Peter Mutharika?

Peter Mutharika lauya ne kuma malami a tsangaya koyar da aikin shari’a.

Bayan komawarsa gida a shekarar 2008 na an nada shi mai ba dan uwansa Bingu wa Mutharika shawara na musaman kan harakokin shari’a lokacin dan uwan na Shugaban Kasa.

Bayan mutuwar Shugaban Kasar a shekarar 2012 wanda ya mutu ta dalilin bugun zuciya ya shugabanci jam’iyyar mai mulki ta DPP daga shekarar 2012.

Sai dai Mataimakiyar Shugaban Kasar ce Joyce Banda ta gaji Bingu wa Mutharika kan ragamar milkin kasar har zuwa shekarar 2014.

A shekara ta 2013, an kama shi bisa zarginsa da shirya makarkashiya don kifar da Shugaba Joyce Banda.

Kotu ta zarge shi da yunkurin boye gawar dan uwansa da kuma hana Mataimakiyar Shugaban Kasar ta gaje shi kamar yadda tsarin mulki ya tanadar.

Ya lashe zaben Shugaban Kasar da aka yi a 2014 da sama da kashi 36 cikin 100 na kuri’un da aka jefa kamar yadda BBC ya ruwaito