✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta wa Chelsea sayen ’yan wasa

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga sayen sababbin ’yan wasa saboda karya dokokin daukar matasan ’yan…

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga sayen sababbin ’yan wasa saboda karya dokokin daukar matasan ’yan wasa da kulob din ya yi.

Hukumar ta ce an karya doka a kan sayen ’yan wasa 29 daga cikin 92 da kungiyar ta dauka.

Haramcin wanda zai kai har zuwa karshen watan Janairun 2020, ba zai hana Chelsea sayar da nata ’yan wasan ba.

Kuma ba zai shafi kungiyar mata ta kulob din da kuma ta kwallon kafar Futsal ba.

Sai dai kulob din ya ce zai daukaka kara kan hukuncin na FIFA.

An kuma ci tarar kungiyar fam dubu 460, inda kuma Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) aka ci ta tarar Fam dubu 390.

Haramcin ya zo ne bayan wani bincike da FIFA ta yi a kan wadansu matasan ’yan kwallo da Chelsea ta saya, har da tsohon dan wasan gabanta Bertrand Traore.

“Mun yi maraba da yadda FIFA ta ce ba a karya doka ba a kan ’yan wasa 63, amma ba mu ji dadi ba kan yadda ta ki yarda da matsayinmu a kan ragowar ’yan wasa 29,” kulob din Chelsae ya bayyana kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wannan hukunci na nufin cewa da wuya kungiyar Chelsea ta sayar da Eden Hazard, domin kuwa zai zama kamar sakin na hannu ke nan, duk da cewa an ruwaito cewa yana shirin barin kulob din ya koma Real Madrid, kuma Real Madrid din tana bukatar sayensa.

Sannan ita kanta Chelsea tana bukatar sababbin ’yan wasa lura da yadda suke a yanzu. A wani bangaren kuma, wannan zai iya hana Zidane zuwa kulob din domin kuwa dole sai ya sayi sababbin ’yan kwallon da yake bukata.

Idan daukaka karar ba ta yi nasara ba, za ta shafi bangarori da dama.