✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An horar da mata da matasa 20 sabuwar hanyar sarrafa masara

Shugaban Sashin Bunkasa Aikin Gona na Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (IAR) Farfesa I U Abubakar ya ce, sun…

Shugaban Sashin Bunkasa Aikin Gona na Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (IAR) Farfesa I U Abubakar ya ce, sun horar da mata da maza 20 kan yadda za su sarrafa masara, kuma mafi yawan wadanda aka horar mutanen Karamar Hukumar Charanci ce a Jihar Katsina.

Ya ce, shirin horarwar wanda aiki ne na dan Majalisar Wakilai daga mazabar Charanchi an yi horarwar a kwana uku ne domin fadakar da su yadda ake sarrafa masara tun daga iri zuwa shuka har yadda za a mayar da masara nau’o’in abinci iri-iri.

Ya ci gaba da cewa, irin wannan horarwar da suka yi tana daya daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya don matasa da mata su samu damar dogaro da kansu.

Farfesa Abubakar ya yi bayanin cewa, Cibiyar IAR ta Jami’ar Ahmadu Bello da Sashin Gudanar da Bincike Kan Tsirrai su horar kan abubuwa 11 da suka shafi masara. Mai sanya ido a kan yadda horarwar ta gudana daga majalisar, Usman Muhammed Mu’azu ya ce, Majalisar Wakilai ce ke daukar nauyin horarwar.

Usman ya ci gaba da cewa, horarwar ta kwana uku ce kan yadda za a sarrafa masara ta fuskoki da dama wanda a Ingilishi ake kira (Balne Chain) kuma wadanda suka samu horon za su koma gida su koya wa wadansu.

Wadansu da Aminiya ta zanta da su dangane da horaon da suka samu sun bayyana gamsuwa kan yadda suka samu horo a zamanance game da yadda za su sarrafa masara, haka kuma sun ce, sun fahimci babu wani abu na yarwa a tattare da masara komai aka gani yana da amfani.