✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An  horar da ’yan gudun hijira dabarun noma irin na zamani a  Toro

Hukumar Tsugunar da ’Yan Gudun Hijira ta Kasa ta shirya wa ’yan gudun hijira 52 da suke zaune a Karamar Hukumar Toro da ke Jihar…

Hukumar Tsugunar da ’Yan Gudun Hijira ta Kasa ta shirya wa ’yan gudun hijira 52 da suke zaune a Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi taron bita.

Taron na kwana biyar ne kan dabarun noma na zamani tare da raba musu kayayyakin aikin noma da suka hada da taki da irin shuka da injinan ban-ruwa da na feshi don su dogara da kansu.

Da yake jawabi a wajen rufe taron bitar, Kwamishinan Hukumar Tsugunar da ’Yan Gudun Hijira ta Kasa, Sanata Bashir Garba Muhammed ya ce saboda damuwar da Gwamnatin Tarayya take nunawa kan halin da ’yan gudun hijirar suke ciki ya sanya ta shirya wannan bita, don tallafa musu.

Ya ce  halin da ’yan gudun hijirar  suke ciki, bai dace a ci gaba da kawo musu shinkafa da garin kwaki suna ci ba. Ya fi dacewa a tallafa musu a koya musu noma irin na zamani, domin su dogara da kansu.

Kwamishinan wanda Mataimakin Darakta a Hukumar, Mista Akintunde Oyasanya ya wakilta, ya yi kira ga ’yan gudun hijirar  su yi amfani da kayayyakin noman da aka ba su.

Ya ce  idan suka yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, gwamnati za ta kara tallafa musu.

A  jawabin shugaban ’yan gudun hijirar na Karamar Hukumar Toro, Alhaji Abdullahi Musa Garkuwa ya yi godiya ga hukumar da Gwamnatin Tarayya, kan wannan tallafi da aka ba su na horar da ’yan gudun hijirar.

Ya ce babu shakka hukumar tana kokari wajen tallafa wa ’yan gudun hijira, domin baya ga wannan tallafin noma, kwanaki ta turo a zo a yi rijiyoyin burtsatse guda bakwai, a wuraren da ’yan gudun hijira suke zaune a karamar hukumar.

Ya ce akwai ’yan gudun hijira sama da dubu 21 a karamar hukumar, wadanda suka fito daga jihohin Bauchi da Filato da Kaduna da Nasarawa da Yobe da Taraba da Adamawa da Borno.

Ya yi  kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da sauran kungiyoyi na ciki da wajen Najeriya, su ci gaba da tallafa wa ’yan gudun hijirar domin su samu su dogara da kansu.